Wannan podcast, mun tattauna kan matsaloli biyu, A yi qoqari a saurara har karshe.
1. Matsalar Shawara
2. Matsalar Aikin Mace
Sau da yawa mutane na fadawa cikin halaka saboda wani shawara da suke samu daga wasu. Aure da yawa sun mutu, jari da yawa sun karye, zumunta da yawa sun yanke duk saboda shawara da a ka basu. Mu kame bakin mu idan mun san cewa ba mu da shawarar da za mu bayar. ba dole sai mun yi magana ba idan bamu da masaniyar al'amura.