Listen

Description

Send us a text

Ranar litinin 19 ga Satumbar wannan shekarar ake sa ran yin jana’iazar Sarauniyar Ingila,  Elizabeth II, wadda ta mulki kasashe 15 shekara 70 da ta yi a  kan karagar mulki. 

Mutuwar Sarauniya Elizabeth II zai kawo sauye-sauye da dama a kasashen 15 da ke karkashin mulkinta, ciki har da sauyin takardun kudi a kasashen.

Saurari cikakken shirin domin sanin irin sauye-sauyen da za su biyo bayan mutuwar ta Sarauniyar.