Listen

Description

Send us a text

Hukumar Nazari da Hasashen Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen cewa a wasu sassan Najeriya za a samu ruwan sama fiye da yadda aka saba da ma ambaliyar ruwa.

Tuni dai aka samu rahoton ambaliyar ta fara barna, inda a wasu wurare ta mamaye gine-gine, ko ta share hanyoyin mota, ko ta tafi da gonaki, ko ma ta yi sanadin mutuwar mutane.

A wannan shiri na Najeriya a Yau za mu duba yadda wasu al'ummu a wasu sassan Najeriya ke kokarin kare yankunansu daga barazanar ambaliya.