Daga cikin abin da ya fi daukar hankali a Najeriya a cikin watan Azumin Ramadan akwai yadda sabbin ma'aurata suka rika zumudi da nuna farin ciki a kafafen sadarwa na samun yin azumi da masoyansu wuri guda a karon farko.
Shin ya ya wadannan sabbin ma'aurata suka yi azuminsu na farko tare da juna?
Shirin Najeriya A Yau ya tattauna da wadansu sabbin aure, ya ji yadda azumin bana ya bambanta da sauran a wurinsu.