Duk da kara wayar da direbobi da fasinjoji da hukumar kiyaye hadura ta tace tana yi, ana kara samun hauhawar wadanda ke rasa rayukansu sakamakon haddura a titin kasar nan.
A shafinta na internet, hukumar kiyaye haddura ta kasa tace a watanni uku na farko na shekarar 2024, mutane 1,471 ne suka rasa rayukansu sakamakon hatsarin mota, kazalika, a watanni uku na farko na wannan shekara ta 2025, adadin ya haura zuwa mutane 1,593 — karin mutum 122, ko kuma kashi 8.3 cikin dari.
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa ake kara samun karuwa rasa rayuka a titunan kasar nan.