A ci gaba da shirye-shiryen zaben 2023, Hukumar Zabe Ta Kasa (INEC) ta bayyana soke rajistar zaben mutum 1,126,359 daga cikin mutum 2, 523,458 da suka yi rajista daga watan Yunin 2021, zuwa 14 ga Janairu na 2022.
Me ya sa hukumar ta soke su, ina makomar wadanda aka soke wa rajista, kuma ta wadanne bangarori matakin na INEC zai shafi zaben 2023 mai karatowa?
Ku biyo mu cikin shirin domin jin amsoshin wadannan tambayoyin da ma wadansu karin bayanan.