A 'yan kwanakin nan, wani abu da ake ganin kamar al'mara, batun satar mazakuta (shafimuleara) ya kara bayyana a tsakanin jama'a.
Shin da gaske ne ana satar mazakuta?
Shirin Najeriya A Yau ya bi diddigin wannan batu, ya tattauna da wani da ake zargin an sace masa mazakuta, kuma ya ji ta bakin likitoci.