Hare-hare a gidajen yari a Najeriya sun karu a Najeriya, inda a baya-bayan na aka kai hari ranar Talata 5 ga watan Yuli a Gidan Yarin Kuje da ke Abuja.
Rahotanni sun nuna cewa 'yan Boko Haram ne suka kai harin inda suka taimakawa yan uwansu tserewa da gidan.
Shirin Najeriya a Yau, ya ji ta bakin 'yan Najriya da masana.