Shin kun san dalilin da ake yin zane-zanen da ke kan hanyoyin titi?
Jama'a da dama, ciki har da wasu matuka sun dauka zane-zanen da ake yi wa tituna kwalliya ce; alhali kowanne daga cikin zane-zanen yana da ma'anarsa, kuma an yi shi ne da nufin kyautata tsarin tafiya a hanyoyin da zimmar kare rayuka da lafiyar matafiya da sauran masu amfani da hanya.
Yau shirin Najeriya A Yau, ya duba yadda masu tuki a Najeriya ke amfani da ka'idojin tuki a kan hanyoyi.