Listen

Description

Send us a text

Nan da kwanaki 7  za a rantsar da sabuwar gwamnati a Najeriya wadda za ta karbi mulki a cikin wani yanayi na kalubalen da sai shugabanni masu kwarewa da sanin makamar aiki za su iya saita kasar da dinke baraka da kuma sake hada kan yan kasar su koma al’umma daya.  

Shirin Najeriya  A Yau ya tattauna da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa da mulki, ya kuma baiwa masana dama sun tofa albarkacin bakin su. A yi sauraro lafiya.