Listen

Description

Send us a text

Rahotanni daga Jihar Borno sun tabbatar da cewa an mayar da tubabbun mayaƙan Boko Haram 6,900 cikin al’umma a bayan dogon lokaci ana yi musu bitar zaman lafiya da sauya musu tunani. 

Anya babu masu tuban muzuru a cikinsu kuwa? 

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya dubi wannan batu, ya ji ta bakin wasu tubabbun mayaƙan Boko Haram da kuma masana harkokin tsaro.