Listen

Description

Send us a text

A cewar masana harkar kiwon lafiya, rashin tantancewa balle a bayar da kulawar da ta dace a kan lokaci na cikin dalilan ta’azzarar barazanar da Zazzabin Lassa ke yi ga bangarori da dama na rayuwar al’ummar Najeriya, musamman a yankunan karkara.


Wani bincike a kan tasirin Zazzabin Lassa a kan rayuwar ‘’yan Najeriya wanda aka wallafa bara a mujallar Springer ya nuna gudunmawar da jahilci yake taimakawa wajen yaduwar cutar a kasar.
A sassan Najeriya da dama dai, ba kasafai mutane ke iya bambance Zazzabin Lassa da sauran nau’ukan zazzabi ba.
Shin yaya za a iya gane Zazzabin Lassa a kuma bambance da sauran nau’ukan zazzabi?


Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.