Listen

Description

Send us a text

 Ranar 8 ga watan Maris ta kowace shekara ce Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar a matsayin Ranar Mata ta Duniya.

Fiye da shekara 100 ke nan ake gudanar da bikin ranar  ta musamman da aka ware wa mata a fadin duniya, domin yaba musu da kuma nuna muhimmancinsu ga al’umma a matsayinsu na uwaye, abokan rayuwa, ’yan uwa da kuma ’ya’ya.

Hakan ya sa wasu magidanta suka jinjina wa muhimmiyar rawar da matansu suke takawa a cikin iyalansu, tare da bayyana wasu hanyoyin da suke yabon matan nasu saboda yadda suke burge su.