Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana 1 zuwa 7 ga watan Agustan kowace shekara a matsayin Makon Shayar da Jarirai Nonon Uwa na Duniya.
Manufar makon ita ce karfafa gwiwar iyaye mata su shayar da jariransu nono, amma taken bikin a bana shi ne "Sahayar da Nonon Uwa Alhaki ne da ya Rataya a Wuyan Kowa".
Shirin Najeriya a Yau zai yi nazari a kan muhimmancin shayar da nonon da kuma rawa da kowa ka iya takawa don ganin komai ya tafi daidai.