Lokacin kaka na zuwa da abubbuwa da yawa, ciki har da tashin wuta a wurare da dama.
da yawa, idan gobara ta tashi, mutane kan rikice, maimakon a taimaki wanda wutar ta kona sai a wayi gari an kara jefa mara lafiyan cikin wahala.
Muna tafe da bayanan me ke kawo gobara da kuma yadda ake taimakon wanda wuta ta kona.