A yayin da ake fama da tsadar rayuwa a fadin duniya, yanzu haka a Najeriya burodi – wanda shi ne abin karin kumallo a kusan kowanne gida – ya zama sai dan wane da wane.
Ko me ya sa haka?
Shirin Najeriya a yau ya binciko mana yadda aka yi aka haihu a ragaya.