An so mai azumi ya fara bude bakinsa da dabino.
Duba da cewa azumin watan Ramadan bai wajabta akan akasarin ‘yan kudancin Najeriya ba, amma duk da haka akwai Al’Ummar Musulmi a cikin su, to ko ta yaya su ke samun dabino domin dabbaka wannan sunnar?
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na tafe da bayanan yadda Musulmin wannan yanki ke samun dabino domin buda-baki.