Damina lokaci ne da dan'Adam yake matukar bukata - da za ta yi jinkiri, sai a ga hankalin kowa ya tashi. A lokaci guda kuma yadda damina kan hana wasu harkoki gudana kan jefa wasu mutane cikin wani irin yanayi..
Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan yadda damina kan shafi rayuwar kananan 'yan kasuwa da masu kananan sana’oi.