Binciken da ya fallasa yadda 'yan siyasa da shugabanni da attajiran Najeriya da wasu kasashe suka azurta kawunansu da kudaden haram na ci gaba da shan fashin baki a fadin duniya.
Shirin Najeriya A Yau zai dubi wannan batu daga tushe domin bai wa mai sauraro damar fahimtar halin da ake ciki game da binciken na 'Takardun Pandora', wanda 'yan jarida masu binciken kwakwaf 600 daga kasashe daban-daban suka gudanar.
A yi sauraro lafiya.