Listen

Description

Send us a text

A lokacin da ake faman yaki da ta’addanci a Najeriya, an kama wadansu ’yan ci-rani dauke da buhunan albarusai da miyagun kwayoyi a wata tashar mota a Jihar Legasa karshen makon da ya gabata. 

Wadanda ake zargin ’yan Arewa ne kuma suna hanyarsu ne kai makaman zuwa yankunansu; Shi me ya sa suka fada wannan muguwar sana’a?

Saurari shirin Najeriya A Yau domin sanin yadda abin ya faru da wadanda aka kama.