Tun ranar 28 ga Watan Yulin 2022 ne yan majalisar dattawan Najeriya na jamiyyun adawa suka fara batun tsige shugaba Muhammadu Buahri, kafin daga bisani takwarorinsu na majalisar wakilai su bi sahun su na ganin an tsige Buhari.
Batun tsige Buhari na daga cikin batutuwan da ke cin kasuwarsu a tsakanin jama'ar kasar.
Shirin Najeriya A Yau ya binciko yadda batun ya samo asali, da kuma halin da ake ciki zuwa yanzu.