Jama'a da dama a Najeriya na kokawa bisa yadda rayuwa ke kara kuntata lokaci bayan lokaci.
Rana zafi inuwa kuna, har wasu ma kan ce jiya ta fi yau, suna kuma tsoron zuwan gobe.
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na tafe da bayanan halin da 'yan Najeriya ke ciki na tsadar rayuwa da matsanancin raunin tattalin arziki, mun kuma tuntubi masana kan hasashen abinda zai biyo baya in aka cigaba da tafiya a haka