Listen

Description

Send us a text

Babban Bankin Najeriya CBN ya saurari korafe-korafen jama’a kan wa’adin daina amfani da tsoffin takardun Naira 1000, 500 da Naira 200 daga ranar 31 ga watan Janairu, inda a yanzu za a daina karbar kudaden daga ranar 10 ga watan Fabarairu. 

Shin ko ta wadanne bangarori wannan matakin na CBN zai shafi tattalin arziki? 

Shirin Najeriya A Yau ya ji ta bakin wadansu ’yan kasuwa, ya kuma ji ta bakin masana harkokin kudi domin jin bangarorin da wannan mataki na CBN zai shafi tattalin arziki.