Yeri Kambari, mai shekaru 40, ya bace ne a shekarar 2014 bayan da jami’an rundunar hadin gwiwa ta Civilian Task Force (CJTF) suka kama shi a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya. Bai shiga kungiyar ta'addanci ta Boko Haram ba. Babu wani abu da ke nuna ya cutar da kowa. Ya tafi gona ne kawai kuma ya kasance abin ya shafe shi. Ya Kodo Alli, yayarsa, ta tuna abubuwan da suka faru kamar sun faru kwanan nan.
Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed
Marubuci: Kunle Adebajo
Muryoyin Shiri: Usman Abba Zanna, Khadija Gidado
Fassara: Rukayya Saeed
Edita: Aliyu Dahiru
Furodusa: Khadija Gidado
Babban Furodusa: Anthony Asemota
Babban Mashiryi: HumAngle Media