A jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, sojoji sun kama dubban mutane ba bisa ka'ida ba a tsakanin shekarar 2015 zuwa 2016 a yunkurinsu na yaki da 'yan ta'adda a lokacin da Boko Haram ke yawaita kai hare-hare. Yawancin wadanda aka kama ba su da laifi. Kaadi Aji yana daya daga cikinsu. Bayan shekaru shida a tsare ba bisa ka'ida ba, a karshe an sake shi ba tare da tuhumar sa ba amma yanzu yana fuskantar wahalar rayuwa.
Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim
Marubuciya: Hauwa Shaffii Nuhu
Muryoyin shiri: Akila Jibrin
Fassara: Zubaida Baba Ibrahim
Edita: Aliyu DahiruĀ
Furodusa: Khadija Gidado
Babban Furodusa: Anthony Asemota
Babban Mashiryi: Ahmad Salkida