Listen

Description

kina gida tare da mijinki da 'ya'yanku hudu, kuna shirya abincin rana kamar kowace rana.

Kwatsam sai kuka ji 'yan ta'adda dauke da makamai sun kewaye garinku. Suna afkawa gidaje, suna sace amfanin gona, suna kashe duk wanda ya musu gadara. Take kuka fita da gudu zuwa cikin daji. Jama'a duk an watse zuwa wurare daban-daban. A wannan yanayi kika nemi mijinki kika rasa, sai bayan lokacin da abun ya lafa, sai aka ce an gano gawar mijinki.

Wajen da kike kira gida yanzu ba tsaro, don haka kuka yi hijira don sake gina rayuwa daga farko.

Amma me farawa daga farko ke nufi?