Zarah na ganin Bama garin al'umma ne mai cike da ban tsoro. A baya, garin ya taba zama cibiyar kasuwanci a jihar Borno. Amma yanzu ya zama tarihi bayan hare-haren da 'yan ta'adda ke kaiwa sama da shekaru goma da suka wuce. Duk da tserewa da ta yi daga sacewa da cin zarafi daga kungiyoyin 'yan ta'adda, amma yanzu yanayi ya tilastawa wannan budurwa komawa garin da ya tara mata bakin ciki hade da rushewar burikanta. Duk da haka, ba ta tsaya da neman ilimi ba.
Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim
Marubuciya:Tracy-Allen Ezechukwu
Muryoyin shiri: Khadija Gidado
Fassara: Ruqayya Saeed
Edita: Aliyu Dahiru
Furodusa: Khadija Gidado
Babban Furodusa: Anthony Asemota
Babban Mashiryi: Ahmad Salkida