Wata ‘yar gudun hijira mai shekara 22 ta shiga hannun ‘yan Boko Haram a lokacin da take sana’ar saro itace. Daga nan suka yi garkuwa da ita.
Ba da daɗewa ba wahalarta ta canja daga garkuwa, zuwa auren dole da ɗan ta’adda, zuwa fyade da samun ciki. Ta kuma yi shaidar yadda ‘yan ta’addar ke yankewa wata wanda ta yi kokarin tserewa kai, wanda har yanzu tunanin wannan tashin hankali ke cikin ranta, duk da cewa ta tsere daga hannunsu bayan shekaru.
Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim
Marubuci: Kunle Adebajo
Muryoyin shiri: Hadiza Sani
Fassara: Zubaida Baba Ibrahim
Edita: Aliyu Dahiru
Furodusa: Abba Toko
Babban Furodusa: Anthony Asemota
Babban Mashiryi: Ahmad Salkida