Listen

Description

Tun bayan da hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce maniyatta aikin Hajjin 2024 su fara neman kafin alkalamin Naira miliyan 4 da rabi, yan ƙasa ke ta cece-kuce kan wannan labari.

Wasu na ganin anya wannan lamari ba zai gagari talaka ba, yayinHda kuma masana da hukumomin ke kare kansu a kan wannan mataki.

A cikin shirin daga laraba na wannan mako mun duba dalilan karin kudin aikin Hajji, da kuma abin da yan kasar ya kamata su duba gameda wannan ƙari