Listen

Description

Jama'a da dama na mamakin yadda 'yan Najeriya basa kishin kasarsu. Shirin Daga Laraba na wannan karon ya bankado dalilan da suka harzuka da yawa daga cikin 'yan Najeriyan har aka wayi gari kasar ta fita daga ransu.

Wasudai na ganin soyayya tana wanzuwa idan kowane bangare na amfana, amma 'yan Najeriya sunce  manyan kasar ba ta su sukeyi ba.
Ayi Sauraro lafiya.