A wannan karon, shirin Daga Laraba ya mayar da hankali ne a kan masu canza wa kan su kama. Masu canza launin fatar jikinsu daga baka ta koma fara. Wato masu Bilichin.
A kashin farkon shirin, mun duba dalilan da ke sa mutane su na canza kamanninsu da Allah Ya halicce su da shi.