Listen

Description

Asabar 12 ga watan Yuni ce Ranar Dimokuradiyya a Najeriya.

Kafin a sauya ranar wannan biki, a da akan yi shi ne ranar 29 ga watan Mayu, ranar da kasar ta koma kan turbar Dimokuradiyya bayan shekaru da dama na mulkin soji.

A bana dai shekara 22 ke nan tun bayan komawa kan tsarin na Dimokuradiyya. 

Ko me wannan tsari ya tsinana wa Najeriya a wadannan shekaru?

Mun tattauna da yan Najeriya a kan cigaban da aka samu; sun kuwa bayyana ra'ayoyinsu sun bayar da shawarwari.