Listen

Description

Yadda ‘ya’yan jamiyyar PDP ke ficewa suna komawa jam’iyya mai mulki na cigaba da nuna yadda take kara samun koma baya a siyasar Najeriya.

Banda haka, rikicin cikin gida da yaki ci yaki cinyewa na cigaba da yi mata dabaibayi.

Shin ko hakan na nufin jam’iyyar ta fara gushewa ne a siyasar Najeriya?

Wannan shine batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari a kai.