Tururuwar da mutane suke yi zuwa manyan biranen Najeriya na barazana ga wadannan alƙaryu ta fuskar tsaftar muhalli.
Misali, wani rahoto da Bankin Duniya ya fitar ya nuna cewa a duk sa'a daya birnin Legas kan yi baƙi 77 – hakan kuma kan haddasa karuwar sharar da ake zubarwa.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan yadda shara ke addabar wasu manyan biranen Najeriya da tasirinta a kan lafiyar jiki da ta muhalli.