Kiyasi ya nuna cewa Najeriya tana asarar sama da dala biliyan 9 a duk shekara sakamakon ayyukan masu hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba, kuma kaso mafi tsoka shi ne fannin zinare.
Rahotanni sun ce hakan na karawa ‘yan ta’adda karfi, inda suke amfani da wannan dama wajen tara muggan makamai a yankin Arewa maso Yamma da ke fama da matsalar tsaro.
'Yan bindigar sun yi ikirarin suna samun kimanin naira miliyan 300 duk mako daga haramtattun wuraren hakar ma’adinai.
Shirin Daga Laraba na wannan makon, bincike ne kan yadda ‘yan ta’adda ke amfani da albarkarun kasa na zinare wajen siyan makamai a yankin arewa maso yamma.