Rashin haihuwa matsala ce da ka iya wargaza gidajen aure musamman a wannan zamani.
Da an samu shekara biyu zuwa uku bayan an daura aure ba tare da an samu karuwa ba za a fara yamadidi da matar a kan ba ta haihuwa.
Sai dai likitoci sun ce maza ma ka iya fama da wannan larura saboda wasu dalilai.
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan wadannan matsalolin da suke hana maza haihuwa.