podcast
details
.com
Print
Share
Look for any podcast host, guest or anyone
Search
Showing episodes and shows of
Ibrahim & Kai
Shows
Najeriya a Yau
Shin Jam’iyyar NNPP Za Ta Kai Labari A 2027?
Send us a textJam’iyyar NNPP wadda Dr. Boniface Aniebonam ya kafa a shekarar 2001, ta samu karfi sosai a Jihar Kano bayan tsohon gwamna Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya shiga cikinta a shekarar 2022 tare da mabiyansa na Kwankwasiyya. Shigowarsa ta farfado da jam’iyyar, inda ta samu gagarumar nasara a zaɓen 2023 ta hanyar lashe kujerar gwamna da wasu kujerun majalisa. Sai dai rikicin cikin gida da rikice-rikicen shugabanci suna ma jamiyyar rauni wanda hakan ya haddasa ficewar wasu manyan ‘ya’yanta zuwa APC, lamarin da ke haifar da tambaya kan makomar NNPP a Kano...
2025-05-16
24 min
Najeriya a Yau
Sabbin Dabarun Hana Matasa Aikata Laifuffuka
Send us a textMasu iya magana kan ce banza ba ta kai zomo kasuwa. Mai yiwuwa hakan ne ya sa matasan da ake zargi da aikata manyan laifuffuka shiga ofishin ’yan sanda, su kuma fita ba tare da wani ya harare su ba, balle ya kama su.’Yan sandan dai sun ce wannan wata dabara ce ta yakar aikata manyan laifuka irin su sata da fashi da makami da kwacen waya da fyade kai har ma da satar mutane don kudin fansa a tsakanin matasa.Ko yaya wannan dabara take...
2025-04-18
25 min
Najeriya a Yau
Dalilan "Farfaɗowar Boko Haram" A Jihar Borno
Send us a textA yanzu haka al’ummar Borno na cikin zulumi sakamakon wasu hare-haren da ake zargin kungiyar Boko Haram ce ta kai a wasu sassan jihar. Wadannan hare-hare dai suna faruwa ne bayan shekaru da dama da ikirarin Gwamnati na cewa an yi nasarar nakasa kungiyar.Ko mene ne dalilin sake farfadowar kungiyar ta Boko Haram a wannan lokaci?Wannan ne batun shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.
2025-04-14
30 min
Najeriya a Yau
Yadda Ake Yi Wa ‘Yan Majalisar Kasa Kiranye
Send us a textMulkin demokradiyya kamar yadda Hausawa ke cewa ‘yancin dan adam.A lokacin da ta baka damar tsayawa don a zabe ka kan wani mukami, kazalika ta baka damar zaben wanda kake so ya shugabance ka kuma ya wakilce ka.Wani abun da demokradiyyar ta baiwa alumma dama a kai kuma shine na yin kiranye ga wakilan da suka zaba musamman idan wadannan wakilan basa biya musu bukatun da suka tura su a kai.Tuni dai alummar kogi ta tsakiya suka fara kada kuri’un kiranye ga sanatar da suka...
2025-03-25
30 min
Najeriya a Yau
Har Yanzu Akwai Masu Rufin Asiri A Najeriya?
Send us a textA tsakanin al’umma akan karkasa mutane gida-gida a bisa mizani na tattalin arziki, musamman a tsarin jari-hujja: akwai mawadata, akwai matalauta.A tsakanin al’umma akwai aji na mutane masu matsakaicin samu wanda ake kira “Middle Class”.Akan saka mutane a wannan aji ne galibi bisa la’akari da aiki ko sana’ar da suke yi, da kudin da suke samu, da matakin ilimin da suka kai, da ma matsayinsu a tsakanin al’umma.Sai dai a baya-bayan nan irin wadannan muntane sun bi sahun matalauta wajen korafi game da...
2025-02-10
25 min
Najeriya a Yau
Dalilin Faduwar Farashin Tumatur A Kasuwa
Send us a textShin mene ne dalilin faɗuwar farashin tumatir warwar a kasuwa? Idan ba a manta ba, a watannin baya farashin Tumatur yayi tashin gwauron zabo wanda aka dade ba’a ga irin sa ba.A wancan lokacin, sai da farashin tumaturin ya kai ga iyalai da dama sun hakura dashi sun koma sayen na gwangwani ko na leda. Wannan ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokacin zai yi nazari a kai.
2025-02-07
27 min
Najeriya a Yau
Yadda "Sojoji Suka Kashe Farar Hula" A Karo Na Biyu A Wata Guda
Send us a textBayanai na kara bayyana game da wani hari da Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta kai a kan wasu kauyuka biyu na Karamar Hukumar Maradun ta Jihar Zamfara, wanda ya yi sanadin mutuwar farar hula akalla 15.Wadanda suka shaida faruwar lamarin dai sun ce sojojin sun kai hari da jirgi mai saukar ungulu ne a kauyukan biyu wadanda ’yan bindiga suka kaiwa hari .Wannan na zuwa ne makonni kusan uku bayan da Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta kai wani harin irin wannan a Karamar Hukumar Silame dake ji...
2025-01-13
24 min
Najeriya a Yau
Halin Da Matsalar Tsaro Ya Jefa Wasu Alummomin Arewa A Shekarar 2024
Send us a textA cikin ‘yan shekarun nan, matsalar tsaro ta kasance babbar kalubale a Arewacin Najeriya. Musamman a jihohin Kaduna, Zamfara, Katsina da kuma jihar Sakkwato. Daga matsalar ‘yan fashi zuwa ta’addanci, yankin ya fuskanci barazanar tsaro daban daban.Duk da irin wadannan kalubale, mutanen wadannan yankuna sun nemo wasu hanyoyi daban-daban na jure irin wadannan matsaloli. Taimakon ‘yan sa kai a wasu al’ummomi ya taka muhimmiyar rawa, inda kungiyoyin sa-kai da kuma tsare-tsaren gwamnati suka yi tasiri a wasu wurare.Shirin Najeriya A Yau zai yi Naz...
2025-01-02
22 min
Najeriya a Yau
Yadda Takkadama Ta Kanannande Siyasar Kananan Hukumomi A Shekarar 2024
Send us a textZabukan Kananan hukumomi na cikin al’amuran da suka dauki hankali a fagen siyasar Najeriya a shekarar 2024.Duk da an gudanar da zabukan cike gurbi a wasu daga cikin jihohin Najeriya, zabukan kananan hukumomi na cikin batutuwan da ’yan Najeriya suka fi zantawa a kai, mai yiwuwa saboda ganin da ake yi cewa wadannan zabukan sun fi shafar alumma kai tsaye.Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi waiwaye a kan kurar da wasu daga cikin zabubbukan kananan hukumomi suka tayar a 2024
2024-12-31
25 min
Najeriya a Yau
Gaskiyar Lamari Game Da Harin Sojoji Kan Al’umma A Sakkwato
Send us a textA baya bayan nan ana cigaba da samun hare hare da sojoji ke kaiwa kan fararen hula kamar yadda wasu suka bayyana.Ko A shekarar da ta gabata, rundunar sojin kasar nan ta kai wani hari garin Tudun biri dake karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna inda harin yayi sanadiyyar mutuwar gomman mutane.Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zaiyi duba ne kan harin da rundunar sojin kasar nan ta kai a jihar Sakkwato
2024-12-27
21 min
Najeriya a Yau
Tasirin Rancen Naira Tiriliyan 138 A Rayuwar ’Yan Najeriya
Send us a textBayan da Majalisar Dattawa ta sahale wa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu karbo wani sabon rance na sama da Naira tiriliyan daya, yawan bashin da ake bin Najeriya ya kai matakin da bai taba kaiwa ba a tarihi. Da wannan amincewa dai yawan bashin da ake bin Najeriya ya kai Naira tiriliyan 138!Wannan shirin na Najeriya a Yau zai yi bincike ne a kan tasirin da wannan bashi yake da shi a rayuwar ’yan Najeriya.
2024-11-22
31 min
Najeriya a Yau
Abin Da Ya Kamata A Yi Da Kananan Yara Masu Zanga-Zanga
Send us a textGurfanar da yaran nan da aka kama watanni uku da suka gabata yayin zanga-zangar ‘#EndBadGovernance’ na ci gaba da yamutsa hazo a Najeriya.Mutane da dama dai, musamman a Arewa, suna ta tofin Allah-tsine a kan kamen yaran, wadanda wasu suke cewa kanana ne, shekarunsu ba su kai a kama su ba ballantana a kai su gaban kotu.Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai tattauna ne kan tanadin doka game da kamen kananan yara, da kulle su, da kuma gurfanar da su gaban kuliya.
2024-11-04
27 min
Najeriya a Yau
Me Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Shaukin Ranar Samun ’Yancin Kai?
Send us a textA duk lokacin da bikin tunawa da Ranar Samun ’Yancin Kai ya zagayo, bisa al’ada, akan ga ’yan Najeriya suna farin ciki.Sai dai a wannan karon alamu na nuna abin ya sauya; ba kamar yadda aka saba gani a shekarun da suka gabata ba, mutane da dam aba su ma san ana yi ba.Shirin Najeriya A Yau zai yi duba ne kan dalilan da suka sa ’yan Najeriya ba sa shauki kamar yadda aka saba gani a da.
2024-10-01
26 min
Najeriya a Yau
Abin Da Ya Sa Ake Ƙara Wa ‘Yan Band A Kuɗin Wutar Lantarki
Send us a textZuwa yanzu masu shan wutar lantarki da ke tsarin Band A sun samu sanarwar kara kudin wutar lantarkiSai dai wasu na ganin ba a iya biyan bukatun da wannan kari ba zai samu muhalli ba Shirin Najeriya a Yau zai tattauna ne kan Dalilin da ya sa ake kara wa masu tsarin Band A kudin lantarki a kai a kai.
2024-07-05
17 min
Najeriya a Yau
Hanyoyin Haɗa Kan 'Yan Najeriya Ta Wasan Ƙwallo
Send us a textFaɗin ƙasa da yawan kabilun da ke Najeriya sun sa zaman 'yan ƙasar uwa ɗaya uba ɗaya masu ƙawazucin juna gagara tun samun ƴancin kai. Ko kun san hanyoyin da ya kamata abi domin haɗa kan ƴan ƙasar wuri guda masu so da ƙaunar juna domin ciyar da ƙasar gaba ta hanyar ƙwallon ƙafa? Lura da goyon baya da fatan alkhairin da 'yan Najeriya suka nuna wa tawagar ƙwallon ƙafar Najeriya a gasar AFCON, mun dubi hanyoyin da za a bi domin samar da ƴan kasa masu haɗin kai da ƙawazu
2024-02-12
15 min
Najeriya a Yau
AFCON: Yadda Za Ku Kauce Wa Bugun Zuciya Yayin Kallon Kwallo
Send us a textRahotanni sun tabbatar da mutuwar 'yan Najeriya uku sakamakon firgita da suka yi bayan an baiwa kungiyar kwallon kafar kasar bugun da ga kai sai mai tsaron gida yayin wasan su da takwararta ta Afirika ta Kudu. Mene ne ke sanya zuciya bugawa har ta kai ga ajali ko mummunan jinya?Mun binciko yadda wadannan bayin Allah suka gamu da ajalinsu yayin kallon wasan, mun kuma ji ta bakin wani likita kan hanyoyin kaucewa bugun zuciya.
2024-02-09
14 min
Najeriya a Yau
Yadda Wata Mata Ta Haihu A Kofar Gida A Mangu Saboda Yaki Bayan Dokar Hana Fita
Send us a textHukumomi a Jihar Filato sun bayyana saka dokar ta baci sakamakon rikicin kabilanci da ya rikide ya koma na addini a karamara Hukumar Mangu amma mahara sun ci gaba da kai hare-hare. Mene ne abin da ya sa har yanzu ba a daina kai hari a Mangu ba? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya binciko halin da ake ciki. ku biyo mu sannu a hankali.
2024-01-25
14 min
Najeriya a Yau
Makomar Ministar Jinkai Betta Edu Da Shugabar NSIP Halima Shehu
Send us a textTun bayan dakatar da ministar jin kai ta Najeriya Betta Edu a jiya Litinin 8 ga Janairu da kuma Halima Shehu daga matsayin shugabar hukumar bada tallafin dogaro da kai ta kasa kwanaki 6 tsakani 'yan Najeriya sun fara bin kwakkwafin wane hali su ke ciki, kuma mene ne abin da ya sa aka dakatar da su? Shirin Najeriya A Yau ya binciko cikakken abin da ake zarginsu, ya kuma ji ta bakin masanin shari'a kan makomar wanda ya aikata abin da ake zarginsu da shi.
2024-01-09
13 min
Najeriya a Yau
Wane Mataki Ya Kamata Mutum Ya Kai Kafin Shekara 30
Send us a textShin kun taba tambayar kanku matsayin da ya kamata matashin da bai wuce shekara 30 ya taka?Da zarar shekaru sun ja ana sa ran a cimma wani buri na rayuwa da zai sa a kalli cewa mutum ya fara samun cigaba da zama cikakken mutum.Shirin Najeriya a Yau ya duba matakin da ya kamata a ce mutum ya kai kafin cika shekara talatin a rayuwa.
2023-12-07
14 min
Najeriya a Yau
Dalilin Dawowar Hare-Haren ’Yan Ta’adda A Arewa Maso Gabas
Send us a textAna murna da raguwar hare-haren 'yan ta'adda a yankin Arewa maso gabas, sai ga shi wasu alamu na nuna akwai yiwuwar wasu na shirin dawo da hannun agogo baya.A 'yan kwanakin nan an samu barazanar kai hare-hare da wasu bayanan sirri a yankunan da ake ganin an ci ƙarfin 'yan ta'addan.Shirin Najeriya a Yau ya duba yadda 'yan ta'adda ke yunƙurin dawo da kai hare-hare a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
2023-11-07
13 min
Najeriya a Yau
Abin Da Ya Sa Hisba Ta Yi Kame A Kano
Send us a textRahotanni daga Jihar Kano sun bayyana cewa Hukumar HISBA ta kai samame wani hotel da kuma wasu gidaje a jihar. Ko mene ne abin da ya sa hukumar HISBA kai wannan samame a wannan lokaci? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya binciko abin da ya sa HISBA ta dauki wannan mataki a yanzu.
2023-11-02
14 min
Najeriya a Yau
Yadda Mazauna Iyakar Najeriya Da Nijar Suka Shiga Ha’ula’i Bayan Rufe Boda
Send us a text’Yan Najeriya mazauna yankunan da ke iyakar kasar Jamhuriyar Nijar na dandana kudarsu sakamakon tsadar rayuwa da tashin gwauron zabon kayan masarufi, tun bayan rufe bodar da Najeriya ta yi a watan Agusta.Anya wannan rufe boda da Kungiyar ECOWAS ta sa aka yi, ba za a ci kai da kai ba?Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya ziyarci garin Illela a Jihar Sakkwato da Maigatari a Jihar Jigawa, da kuma Kwangalam da Jibiya a Jihar Katsina, domin jin halin da mazauna garuruwan suka tsinci kansu a ts...
2023-10-19
14 min
Najeriya a Yau
Gwagwarmayar June 12 A Dimokuradiyyar Najeriya
Send us a textYau rana ce ta demukradiyya a fadin kasar Najeriya, wato goma sha biyu ga watan Yuni da kowa ya sani da June 12.An sha fama da gwagwarmaya kafin a kai ga yin zabubbukan ranar 12 ga watan Yunin shekarar 1993 da gwamnatin mulkin soja ta Ibrahim Badamasi Babangida ta soke.Shirin Najeriya a Yau ya tattauna da masanin harkokin siyasa da ya yi cikaken bayani tare da bayar da tarihin abinda ya faru.A yi sauraro lafiya.
2023-06-12
15 min
Filmmaker Wannabees Podcast
S02 #58 Why YouTubers Outshine Brands in Holding Attention?
Back in the day, in the age of television. Brands and advertising companies Held the attention, they were the gate keepers and had the power. In today’s world, things are a little different. The power has shifted to the hands of the creators, YouTubers, Instagrammers & Tiktokers. What has caused this shift? How can brands take advantage of that? And what are they missing out on?
2023-04-20
23 min
Filmmaker Wannabees Podcast
S02 #57 Behind The Scenes: Keys to Great Producing In Film and Commercials W/ Karim Gad
We were fortunate to have Karim Gad on this episode, an avid and experienced producer in Qatar. To talk about it all. The journey, the setbacks, the wins, the fun along the ride and the lessons. Key aspects of producing. We answer lots of questions like what is the difference between a production manager and a producer? What makes a good producer? How do you maintain a sustainable career as a producer? And lots of fun and interesting stories. Please tune in till the...
2023-04-12
49 min
Filmmaker Wannabees Podcast
S02 #56 Here's Why You Shouldn't Make Your Video Ads Look Perfect
Today we will be talking about a few thoughts on why making a video ad look perfect could potentially harm your brand. We will discuss our definition of a perfect looking video ad, as well as the times when we must make a video look perfect, super clean and polished.
2023-04-06
18 min
Filmmaker Wannabees Podcast
S02 #55 How is Artificial Intelligence Manipulating Truth in Real Time?
What is real? Daily tools and devices that we use in our lives are manipulating truth without us knowing. So, can we depend on them? Years down the road, when AI has captured and recorded us in perfect and beautiful shapes, how will that impact the next generation? What does this mean for the average filmmaker? Some thought provoking questions that we try to explore in this episode. Hope you enjoy it!
2023-03-29
18 min
Filmmaker Wannabees Podcast
S02 #54 Limiting Beliefs Filmmakers have
In this week's episode, we talk about some of the limiting beliefs that we had as filmmakers when we first started out. We also discuss some trends and ideas that hinder filmmakers from moving forward.
2023-03-22
29 min
Filmmaker Wannabees Podcast
S02 #53 Chat GPT: Filmmakers Perspective & Discussion
Hello everyone! We are Back! Season two of the podcast with new structure, new topics and fresh perspectives. Today's episode is about the one and only Chat GPT and a little bit of it's likes of AI Softwares. In what ways have they changed the filmmaking industry? What does this wave of AI mean for the average filmmaker? And what can utilise them for? Hope enjoy the discussion and many more are on the way!
2023-03-15
24 min
Najeriya a Yau
Fadi-Tashin Gwamnoni Don Cin Zaben 2023
Send us a textGwamnonin da jam’iyyunsu ba su kai bantensu a jihoinsu ba a zaben shugaban kasa na fadi-tashin ganin ba a maimaita hakan ba a zaben gwamna da za a yi Ranar Asabar 11 ga Maris. Anya wannan farga da gwamnonin suka yi bazata zama fargar jaji ba? Shirin Najeriya A Yau ya dubi yadda gwamnonin da jam’iyyarsu ta fadi a jihohinsu a zaben shugaban kasa ke tunkarar zaben gwamna da ke tafe idan Allah Ya kai mu.
2023-03-09
15 min